WANI MUHIMMIN LAMARI DA KE KUSANTO MU

image_20180204_221820.jpg
Daga MusaddieeQ AshaheeD.

Da farko dai ita tarzoma fitina ce, ita kam fitina Allah ya tsinewa (La'anci) mai ta da ita.

Sanin kowane mazaunin jihar Kano ne cewa zaben kananan hukumomi na kusantowa ta in da bai wuce kwanaki kalilan ba a gabatar da shi.

Jan hankali na bai wuce kan matasa ba da ake amfani da su wajen tayar da tarzoma, ta yadda 'yan siyasar mu ke basu kwayoyi da kuma rarraba musu makamai domin su haddasa hargitsi, shi fa mulki amana ne da ya dace shugabanni su kula da girman sa.
Wani hadisi da ya inganta daga Manzon Allah (s.a.w) cewa: "Dukkanin ku makiyaya ne (masu kiwo ne), kuma dukkanin ku ababan tambaya ne game da kiwon da Allah ya ba ku" sai ya soma da shugaba, in da yace: "Shugaba mai kiwo ne, kuma sai an tambaye shi akan kiwon da aka ba shi".

Dole shugabanni su kula da wannan babban hakkin da al'ummah ke da shi akan su, dole ne su ba su kulawa ta musamman da zai inganta rayuwar su, misali shugaba ya san da cewa ko da mutum bai zabe shi ba, to akwai hakkin sa akan sa, na sai ya kare.

  • Lafiyar sa
  • Rayuwar sa
  • Dukiyar sa, da ma.
  • Mutuncin sa.
    Wannan hakki ne da ke kan shugaba, da sai an tambaye sa yadda ya tafiyar da mulkin sa.
    Za a tambayi shugaba ta yaya akai yaci ya koshi, amman kuma talakawa suka kwana da yunwa.
    A tambaye sa dalilin yadda akai matar sa ta ci ta koshi amman matan talakawa suka kwana da yunwa.
    Haka ma game da yadda 'ya'yan shugaba suka ci suka ci suka koshi, amman kuma 'ya'yan talakawa suka kwana da yunwa.

Wa ta rana Sayyadina Umar (RA) ya ji wa ta tsohuwa tana fadawa yar ta cewa ba su da ko kwayar abinci da zasu ci, sai ya fashe da kuka, yace: " Daman a mulkin sa akwai wanda zai wuni bai ci komai ba? Sai ya sanya aka wadata su da kayan abinci, wanda zai ishe su tsawon lokaci.
Shin a wannan lokacin mutane nawa suka kwana suka tashi ba su da abinci?
Wanda Khalifa Umar Bin Abdul Aziz yake cewa matar sa, ranar da aka damka masa mulki taga yana ta kuka, sai tace: 'Kai da zaka yi murna an zabe ka a matsayin shugaba, amman kuma ka kasa barci, kake kuka? Shi ne yace ma ta: "Yana kuka ne saboda a daren nan akwai Mafatauci a daji yana jin sanyi, da bai san a ina yake ba, kuma sai an tambayesa me yasa bai kai masa bargo ba?
Bai san adadin talakawan da basu da abinci ba, kuma sai an tambayesa me yasa suka kwana da yunwa bai kai musu abinci ba?
Hatta dabbobin da suke yawo acikin kasa sai an tambaye ni akan su, wannan shi ne dalilin da ya sa ni kuka"

Za a tambayi shugaba ga me da ingantacciyar hanya, shin ya samar da ita ta yadda ko da dabbobi ne sun bi ta ita ba tare da samun gargada ba?
Ba zan manta kissar sayyadina Umar (RA) a lokacin yana khalifanci, yana kuma garin madina.
Wa ta rana ya ga Alfadari/doki yayi tuntube a hanya, sai ya fashe da kuka, sai 'yan majalisar sa suka tambaye shi, saboda Alfadari yayi tuntube kake kuka?
Sai ya basu amsa da cewa: "Ina tsoron Allah ya tayar da ni a ranar Lahira, ya tambayeni ta yaya akai alfadari yayi tuntube a kasar Iraqi? Ban gyara hanya ba yayi tuntube.
Duk da cewa shi fa Sayyadina Umar yana Madina, amman yake tsoron lamarin hanya a kasar Iraqi.
Ba fa ma mota ba taje ta yi karo da fa mutane har ta kai su ga rasa rayukansu.
Shin shugaba ya san da wannan a game da lamarin kyakkyawan shugabanci, wajen kulawa da hanyoyi tare da inganta su?
Batun haraji da ake karba daga hannun mutane fa?
Shin ana biyan albashin ma'aikata akan lokaci da kuma dadin rai?
Shin masu karbar fansho fa, ana basu hakkokin su akan lokaci?
Shugaba fa ya san hakki ne babba da ya dace ya sauke, yaya akai yayi barci cikin jindadi da kwanciyar hankali, amman kuma talakawa suka kwana a firgici da tashin hankali? Sai an tambaye sa akan wannan.
Sai kuma an tambayi kowane shugaba adadin zubda jinin da akai a mulkin sa, ko da ba lokacin sa aka faro ba shima kansa samu yayi ana yi, to dole sai ya samar da aminci a wajen da ake hargitsin.
Shugaba ya sani idan kafin ya hau mulki nauyin iyalin sa ne kawai a kansa, to ya sani daga ranar da aka rantsar da shi akan kujerar mulki aka bashi kundin tsarin mulki, to ba nauyin iyalin sa kadai ba ne ya hau kansa, duk sauran jama'ar da yake mulka sun zama iyalin sa, sai an yi musu hisabi a ranar tashin alkiyama.

A lokacin sayyadina Umar Bayahude ya tsufa tukuf baya iya biyan haraji har sai yaje yayi dako, amman yace: "A bashi albashi" duk da ba addinin su daya ba.
Wa ta rana sayyadina Umar (RA) ya ga tsohon bayahuden ya fita dako, sai sayyadina Umar ya tambaye sa: "Kai kuma ina zaka tsofai tsofai da kai ina zaka je?" Sai yace: "Zan je in yi dako ne in nemo kudi, dan in samu in biya haraji"
Sai sayyadina Umar (RA) yace da shi: "Bamu yi maka adalci ba idan muka ci kuruciyar ka, kuma muka kyaleka, muka tozartar da kai bayan ka tsufa".
Sai sayyadin Umar ya sa ake biyan sa.

Shin ya batun hakkokin mutane da ke kan shugaba yana sauke su yadda ya kamata?

A lokacin Umar Bin Abdul-Azeez jika a wajen sayyadina Umar (RA) yayi khalifanci, sai da ta kai akuya da kura suna yin kiwo waje daya ba tare da kurar ta taba akuyar ba, saboda adalcin mulkin sa.
Sai da ta kai babu talakan da zai wayi gari ba tare da akwai tulin kayan abinci ba a gidan sa, har ta kai ba talakan da zai karbi zakka, sai dai a tura ta baitilmalin gwabnati.

Shin shugabanni sun cika alkawuran da suka daukar wa talakawa a yayin gangamin yakin neman zabe?
Shi kuma fa abin tambaya ne a ranar Alkiyama, kamar yadda Allah ya fada cewa: " Ku cika alkawari domin alkawari abin tambaya ne".

Dukkanin wasu rikice rikice da suke faruwa gwabnati na da damar dakatar da shi ta hanyar maslaha ko tsaurara matakan da suka dace.
Mu dauki kawai rikicin makiyaya da ya addabi jihohin Taraba, Jos da Benue, da shi yake gudana a wannan lokaci, shin wane irin matakai gwabnati ta dauka na dakile wadannan fitintinun?
Shin ina sojin gonan da aka kama?
A kwanaki ne rundunar sojin Najeriya ta 3 battalion ta kama wasu yan bindigar sa kai su tara da sukai ikrarin suna aiki ne a matsayin civilian JTF a garin Arefo da ke iyakar jihohin Taraba da Benue, kuma lokacin da aka kama su, biyar daga ciki suna dauke da bindigogin AK47 cike da alburusai, wanda suka samu horarwa daga tsoffin jami'an tsaro, wanda suka tabbatar da gwabnati ne ke daukar nauyin su, wanda an ce fiye da 700 cikin dubu na mutanen da aka horar akan haddasa rikice rikicen fulani da manoma dinsuna dauke da manyan makamai ne, kuma an tabbatar da ba fulani ba ne.
Shin wane mataki gwabnatin tarayya ta dauka domin tabbatarwa da al'umma ba fulani ba ne ke kashe wadannan rayukan a jihohin uku?
Shin wanne mataki kuma gwabnatin ta dauka akan gwabnatin da suke daukar nauyin wadannan azzaluman mutanen?
Ba abin kunya ba ne ga gwabnati da ta yi shiru a game da lamarin rikicin jihohin biyu?
Idan lokacin zabe ya zo maimakon shugabanni su fita su nemi ra'ayin jama'a su duba cancantar su, sai su shugabannin su zauna su shirya barna mummuna, da su shirya cewa ranar zabe kudi nawa zasu ba wa ma'aikatan zabe dan su shirya rashin gaskiya, kudi nawa zasu ba wa jami'an tsaro dan idan sun ga ana barna su kawar da kawunan su, sai shugabanni su baiwa matasa kwayoyi domin su haddasa rikici tare da hargitsa gari, ayi ta kone kone domin shugabanni su kawar da hankulan mutane daga magudin da shugabannin suka shirya.

Ya dace matasa su gane cewa wadannan shugabannin da suke raba musu kayan maye, kawai suna amfani da kwakwalensu ne, kuma su makiyan su ne, su yi tunanin shin mai yasa ba 'ya'yan su a lokacin da ake gudanar da rikicin?
Me yasa ba matan su a yakin neman zabe?
Kayi tunani mai zurfi dan uwa, me suka tsinana maka da kai da ahlin ka bayan hawan su?
Me ya sanya suka ki sama maka ingantacciyar rayuwa, wajen baka kyakkyawan ilmi, amman kuma 'ya'yan su suna can suna karatu a manyan makarantun kasashen waje da kuma rike da manyan mukaman gwabnati, da yin aiki a matsayi mai nagarta.
Kai me yasa suka hana ka samun kyakkyawar rayuwa irin wacce suka samarwa 'ya'yan su da matan su?
An ya kuwa kana hankalta dan uwa?
An ya kuwa kawai ba wasa suke da kwakwalen mu suke ba.

A karshe zan rufe da wani hadisin Manzon Allah (s.a.w) da yake fadar cewa ku guji abubuwa biyar tun kafin masifu biyar su same ku, a in da a ciki ne yake fadar cewa: "Matukar shugabanni ba su daina cin amana, da zalunci ba, suka cigaba da fasikanci, to da sannu Allah zai turo fitintinu masu bibiyar juna".

image_20180204_222040.jpg

DQmTQcetbhCRqJbD6DQMcNoU8vRsWucxCP976vYDSwwohwz.jpeg

Sort:  

I really don't understand the language but am sure it gonna be good and nice..... Hope to received an upvote from it.

Its Hausa language, thanks for viewing.

You welcome boss.... I would be greatful if you can upvote me

Coin Marketplace

STEEM 0.04
TRX 0.33
JST 0.101
BTC 64135.15
ETH 1820.07
USDT 1.00
SBD 0.38